29 Afirilu 2021 - 14:01
Shugaba Bazoum Mohamed, Ya Gana Da Jakadan Iran A Nijar

Shugaba Bazoum Mohamed, na jamhuriyar Nijar, ya gana da jakadan jamhuriyar Musulinci ta Iran a birnin Yamai, a ranar Laraba.

ABNA24 : Yayin ganawar, jakadan na Iran, M. Mehdi Karoust, ya tabo batutuwa da dama da suka shafi dadadiyar alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Iran, ta kasance kasa mai kusanci da Nijar na tsawon shekaru, kuma tana fatan taimakawa kasar a fannoni da dama, a cewar jami’in diflomatsiyan na Iran.

A game da batun da ya shafi bada ilimi, Iran, na da jami’a a birnin Yamai mai dalibai 500 wadanda Iran ke daukar nauyin karatunsu, wanda kuma a cewarsa kasar na son taimakawa jami’ar domin ta shahara a duniya.

Ya kuma ce a shirye Iran ta ke, ta taimakawa Nijar a wajen koyar da ayyukan hannu domin shawo kan matsalar rashin aiki yi dake damun matasa.

A sha’anin kiwon lafiya kuma jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta ce tana tunannin canza fasalin asibitin da take da shi a Yamai, zuwa na kwararu domin ya zama na kasa da kasa.

342/